Labarai
Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 9 a Kano

Dakarun rundunar Sojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga tara a wani artabu da aka yi a ƙauyukan Bakaji da Unguwar Garma, a yankin Goron Dutse na Karamar Hukumar Shanono a Jihar Kano.
Sai dai a yayin fafatawar, wani ɗan sa-kai, ya rasa ransa yayin da aka jikkata wani guda.
Shugaban tsaron Al’umma a yankin na Shanono da Bagwai, Yahya Bagobiri, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari ne da daddare, in da aka kwashe tsawon sa’o’i musayar wuta. Duk da dauki ba dadin da sojoji suka yi, ‘yan bindigar sun sace shanu kimanin 40 tare da yin garkuwa da mutane shida, sai dai an kashe tara daga cikinsu, kuma sun gudu sun bar babura da dama.
Rundunar ta yabawa jajircewar dakarun da suka kare yankin, tana mai jaddada ƙudurin ci gaba da murƙushe ‘yan bindiga domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login