Connect with us

Kiwon Lafiya

‘Yan bindiga sun kashe sojoji 9 na rundunar Operation Cat Race a Kaduna

Published

on

‘Yan bindiga sun kashe wasu sojoji Tara da ke cikin rundunar dakarun Operation Cat Race a yankin karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ramuwar gayya ne sakamakon kisan gillar da sojoji suka yiwa shugaban su a kwanakin baya mai suna Buhari wanda aka fi sani da Buharin Daji.

Jami’an tsaro ne dai suka kashe Buharin Daji yayin wani ba ta kashi da suka yi a jihar Zamfara makwanni biyu da suka wuce.

Sai dai har zuwa yanzu rundunar sojin kasar nan ba ta fitar da sanarwa kan batun ba, yayin da ana sa bangaren gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya mika da sakon ta’aziya ga iyaye da kuma ‘yan uwa da abokan arzikin mamatan.

Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe takwas zuwa tara a kauyen Kampani da ke yankin karamar hukumar Birnin Gwari.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,434 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!