Labarai
Sojoji sun sanar da mutuwar shugaban ISWAP Al-barnawiy
Rundunar sojin ƙasar nan ta sanar da rasuwar jagoran ƴan ta’addar ISWAP Abu Mus’ab Al-barnawiy.
Babban hafsan tsaron ƙasar nan Janar Lucky Irabo ne ya sanar da hakan ranar Alhamis a wani taron manema labarai a Abuja.
Sashin Hausa na RFI ya rawaito cewa Janar Irabor bai yi bayanin lokaci ko yanayin da aka kashe Al-barnawiyn ba.
Har kawo yanzu dai ƙungiyar ta ISWAP ba ta ce komai ba kan lamarin.
Tun bayan mutuwar jagoran Boko Haram Abubakar Shekau ne Al-Barnawi ya ci gaba da jan ragamar ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso gabashin ƙasar nan, da yankunan Tafkin Chadi.
Duk da fuskantar hare-hare daga wasu ƴan tsagin Boko Haram da suka ƙi yi masa mubaya’a.
Sashin Hausa na RFI ta rawaito cewa ,fiye da mutane dubu 40 ne hare-haren Boko Haram ya hallaka daga 2009 zuwa yanzu, yayin da mutane fiye da miliyan biyu suka rasa matsugunansu.
You must be logged in to post a comment Login