Ƙetare
Sojoji sun yi barazanar juyin mulki a kasar Benin

Wasu rahotanni masu tushe daga ƙasar Benin sun tabbatar da cewa an fara yunƙurin juyin mulki da safiyar yau Lahadi, inda ake zargin sojojin da kai hari a gidan shugaban ƙasar Patrice Talon da ke Porto-Novo.
Kamar yadda kafar yada labarai ta France24 ta ruwaito, sojoji ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanar Pascal Tigri sun karɓe iko d tashar talabijin ta ƙasa, suka kuma bayyana cewa sun “hambarar da Talon daga mulki.”
Har yanzu dai ana ci gaba da sa ido don samun cikakken karin bayani a nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login