Connect with us

Labarai

Sojoji sun kashe ƴanbindiga 45 a jihar Katsina

Published

on

Sojojin ƙasar nan sun kashe ƴanbindiga 45 da suka kai hari wani ƙauye a jihar Katsina da ke arewacin ƙasar.

Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da maraice kamar yadda hukumomin jihar suka tabbatar.

Rahotonni sun ce tun da farko ƴanbindigar waɗanda suka taso daga jihar Zamfara mai makwabtaka, sun kai hari ƙauyen Alhazawa na ƙaramar hukumar Danmusa a ranar Alhamis domin satar shanu.

To sai dai mazauna garin sun nuna turjiya inda suka kashe huɗu daga cikin maharan.

Kwana guda bayan hakan ne kuma ƴanbindiga suka sake taruwa da nufin ɗaukar fansa kan mazauna ƙauyen, inda suka ci karo da sojoji a kan hanyar tasu, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakani.

Bayanai na cewa an kashe sojojin ƙasar uku a lokacin gumurzun.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!