Labarai
Sokoto: Ƴan sanda na shirin hana amfani da motoci masu duhun Gilashi

Rundunar ƴan Sandan Jihar Sokoto, ta sanar da cewa daga ranar Alhamis, 2 ga watan Oktoba bana, za ta fara aiwatar da doka ta hana zirga zirga ga motoci masu amfani da bakin gilashi wato TINT ba tare da lasisi ba, bayan ƙarewar wa’adin sassauci da aka bai wa direbobi a bisa dokar shekarar 2004.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Ahmad Rufai, ya ce duk masu motocin da ke buƙatar lasisi dole su kammala rajistar su ta hanyar shafin hukumar ta possap.gov.ng kafin fara daukar wannan mataki.
Haka kuma, ya gargadi jama’a da su yi hattara da masu yaudara da za su iya amfani da wannan tsari don amfana da kansu.
Rufai ya bayyana cewa tsarin neman lasisin yana buƙatar amfani da lambobin NIN da BVN ko TIN wajen buɗe asusu tare da tabbatar da shi sai shigar da bayanan mota da ɗora takardu da biyan kuɗi kafin ƙarshe a tabbatar da shi ta hanyar bincike da ɗaukar bayanan yatsa.
You must be logged in to post a comment Login