Connect with us

Labarai

Za’a fara rataye masu garkuwa da mutane a Katsina

Published

on

 

Rundunar ‘yansadan ta  jihar Katsina, ta ce za fara rataye masu garkuwa da mutane nan ba dadewa ba.

Kakakin rundunar ‘yansandan ta jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka a wata takarda da ya sakawa hannu  aka rabawa manema labarai.

Takardar ta kara da cewa, ta bankado wani makarci  da wasu batagari, ke amfani dashi ta hanyar kiran al’umma ko tura sakon kar ta kwana da cewar an yi garkuwa da ‘yan uwansu tare da yin kira gare su da su hanzarta biyan wasu makudan kudade ko a yi garkuwa dasu ko wasu daga cikin dangin su.

labarai masu alaka.

An kashe barayin shanu da masu garkuwa da mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama masu garkuwa da mutane 93

 

Don haka rundunar take gargadi da kakkausar murya ga masu aikata hakan cewa doka zatayi aiki a kansu kamar yadda ta tanada.

Hukumar ‘yansandan tace al’umma su sani cewa sashen doka na jihar Katsina, ta garkuwa da mutane wacce akayi wa kwaskwarima sashe na dari biyu da arba’in da uku, ya tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk mai aikata garkuwa da mutane.

Hukumar ta kuma umarci iyaye da su saka ido a yankunan su da zirga zirga ta bakin  fuskoki ko abinda basu aminta dashi ba kasancewar doka zata yi aiki akan duk wanda aka samu da laifi ba sa ni ba sabo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,216 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!