Labarai
Soyayya ruwan zuma : Budurwa ta aikewa saurayin ta ‘yan fashi a Kano
Kotun majistiri dake zamanta a Gyadi Gyadi karkashin mai sharia Auwal Yusuf ta dage sauraron karar wata mace mai suna Fatima Umar wadda ake zargi da aikewa tsohon saurayin ta ‘yan fashi da makami gida tare dayin awon gaba da kudade sama da naira dubu dari takwas saboda yaki auren ta.
Lamarin ya faru ne a kwanakin baya inda tsohon saurayin nata Abdulhadi Shuaib suka dauki lokaci mai tsaho suna soyayya da Fatima Umar, daga bisani kuma Abdulhadi yayi adduar neman zabin All..h akan auren nasu daga baya yace ya hakura da auren.
Sai dai daukar wannan mataki da Abdulhadi Shuaib yayi baiwa Fatima dadi ba wanda hakan yasa ta turo masa da gungun ‘yan fashi da makami har cikin gidansa kamar yadda ya shaida mana a yau bayan kammala zaman kotun.
Barista Anas Idris Baba shine lauyan mutane uku daga cikin wadanda ake zargi yace tun a zaman kotun na baya sun bukaci kotu data basu belin wadanda ake zargi da aikata wannan laifi.
Sai dai duk kokarin da mukayi domin jin tabakin lauyoyin gwamnati akan lamarin amma sunki cewa komai.
Wakilin mu na Kotu da ‘yan sanda Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito mai sharia Auwal Yusuf na cewa kotu zatayi nazari akan bukatar da lauyoyin bangarorin biyu suka gabatar mata, inda kotu ta sanya ranar ashirin da hudu ga wata mai kamawa domin cigaba da shariar.
You must be logged in to post a comment Login