Manyan Labarai
SSANU da NASU za su tsunduma yajin aikin mako 2
Haɗakar ƙungiyoyin manyan ma’aikatan jami’o’ i SSANU da na ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba ta ƙasa NASU sun yi barazanar tsunduma yajin aikin makwanni biyu.
Yajin aikin nasu dai na wani mataki na jan hankali gwamnati kan ta cika musu alƙawarin su.
Sakataren ƙungiyar NASU Mr Peters Adeyemi ne ya bayyana hakan a wani zama da su ka yi da shugaban ƙungiyar SSANU Muhammad Ibrahim a Abuja.
Ƙungiyoyin sun ce har yanzu gwamnatin tarayya ba ta cika musu alƙawarin kuɗaɗen alawus alawus ɗin da ta ce za ta basu ba, da ya kai sama da Naira biliyan 22.
Mr Peters Adeyemi ya ce hakan ya sa suka yi taron haɗin gwiwa tare da rubutawa ministan ƙwadago da samar da aikin yi Chris Ngige takarda domin yin gargaɗi.
Ta cikin takardar da ƙungiyoyin suka aikewa ministan sun ce ya zama wajibi gwamnatin ta biya kuɗaɗen alawus alawus ga ma’aikatan su.
You must be logged in to post a comment Login