Labarai
SSANU da NASU za su tsunduma yajin aikin makwanni biyu
Kungiyoyin manyan ma’aikatan jami’ar Bayero da ke nan Kano wato SSANU da na NASU sun yi kira ga mambobinsu da su fara gudanar da yajin aikin gargadi na tsawon makonni biyu kan kin biya musu wasu bukatunsu da gwamnatin tarayya ta gaza yi musu.
Shugaban kungiyar SSANU kwamared Haruna Aliyu ne ya bayar da umarnin tafiya yajin aikin yayin taron da kungiyar ta gudanar kan umarnin da babbar kungiyarsu ta kasa ta bayar na tafiya yajin aikin gargadin na makwanni biyu.
Kwamared Haruna Aliyu, ya kuma ce kungiyar na bukatar gwamnatin tarayya da ta biya musu wasu bukatunsu guda takwas, da suka hadar da fita daga cikin sabon tsarin albashi na IPPIS, da rashin biyan ‘ya’yan kungiyar alawus-alawus dinsu da ma rashin baiwa ‘ya’yan kungiyar mukaman da suka dace.
Da yake tsokaci kan tafiya yajin aikin, shugaban kungiyar NASU reshen jami’ar ta Bayero kwamred Abdullahi Nasiru Abdulrafi’u, cewa ya yi yajin aikin gargadin da kungiyoyin suka tafi ya shafi duk wani ma’aikaci dake karkashinsu da suka hadar da ma’aikatan asibiti da jami’an tsaro.
Wakilinmu Abubakar Tijjani Rabi’u ya rawaito cewa kungiyoyin sun kafa kwamiti na musamman da zai rinka zagayawa dukkan wuraren aikin da ‘ya’yan kungiyar ke yi domin tabbatar da tafiya yajin aikin gargadin na makonni biyun da aka umarce su.
ATR/AMA
You must be logged in to post a comment Login