Labarai
SUBEB ta yaba da yadda Musa baƙar Kano ke gudana

Hukumar kula da ilimin bai-daya ta jihar Kano SUBEB, ta nuna gamsuwarta kan yadda musabakar karatun Al-Qur’ani Mai tsarki ke gudana a kwanakin nan.
Shugaban hukumar Alhaji Yusuf Kabir, da ya samu wakilcin babban jami’i a hukumar Malam Magaji Yusuf, ne bayyana hakan a Litinin ɗin makon na yayin da aka shiga rana ta biyar da fara musabakar.
Ya kuma yaba da kokarin kwamitin amintattu na musabakar Al-Qur’anin na jihar Kano bisa yadda suke gudanar da ayyukansu.
Da ya ke ganawa da manema labarai, Alhaji Sabiu Bako mamba a kwamitin shirya musabakar ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta ƙarasa samar da kyautukan da za a raba wa zakarun da za su samu nasara a musabakar, kafin ranar da za a kammala.
Yanzu haka dai, an shiga ɓangare na izu sittin tare da Tajawidi a fannin maza.
You must be logged in to post a comment Login