Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Sunshine Stars: Ba zamu dawo ba sai an biya mu albashi – ‘Yan wasa

Published

on

‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Sunshine Stars sun kauracewa sansanin daukar horo sakamakon rashin biyan su albashin watanni biyar.

Hukumar gudanarwar kungiyar ta umarci ‘yan wasan da su dawo sansanin daukar horo don shiryawa gasar cin kofin kwararru ta NPFL ta 2020/2021 da ake shirin farawa nan gaba kadan.

Rahotanni na cewa babu ko mutun daya daga cikin ‘yan wasan da yayi biyayya ga umarnin hukumar kungiyar, suna masu cewa sai an biya su albashin da suke bi a baya.

Mai horas da kungiyar ta Sunshine Stars Gbenga Ogunbote ya ce yana fatan ‘yan wasan zasu dawo sansanin nasu don tattaunawa da hukumar gudanarwar kungiyar.

Ogunbote ya ce “Yanzu haka gwamnatin jihar ta Ondo ta amince da fitar da kudin albashin ‘yan wasan na watanni hudu daga cikin na watanni biyar da suke bin kungiyar, saboda haka za a biya su nan bada dadewa ba”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!