Connect with us

Labaran Wasanni

Super Eagles za ta fafata da Côte d’Ivoire da Tunisia

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles za ta kara da kasar Côte d’Ivoire da kuma Tunisia a wasannin sada zumunta na kasa-da-kasa a watan Oktoba mai zuwa.

Najeriya dai za ta fafata da kasar Côte d’Ivoire a ranar 9 ga watan na Oktoba, kafin daga baya su hadu da kasar Tunisia bayan kwanaki 4.

Shugaban hukumar NFF, Amaju Pinnick, ya ce, za’a gudanar da wasannin guda biyu ne a kasar Austria.

Shugaban, ya ce, “Hukumar ta ci gaba da tattaunawa wajen ganin an samu damar wasannin sada zumunta, tsakanin Najeriya da wasu kasashen, sai kuma gashi an samu damar yin wasan sada zumunta har guda biyu, duk da cewa muna jiran gwamnatin tarayya ta bayyana ranar da za’a dawo a ci gaba da wasanni a fadin kasar nan”.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!