Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Super Eagles za ta kai gasar kofin duniya- Amaju Pinnick

Published

on

Shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa NFF Amaju Pinnick ya ce ya nada tabbaci tawagar Super Eagles ka iya buga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 a kasar Qatar.

Pinnick ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter jim kadan bayan ganawa da mambobin hukumar a birnin London.

Najeriya dai na shirin fafatawa da kasar Ghana a wata mai kamawa, wanda hakan zai bawa kasashe biyar damar buga gasar da sune zasu wakilci nahiyar afrika a gasar.

“Duka wani shiri da zamuyi mun kammala, bayaga a gefe guda muna kara yin wasu ta karkashin kasa na ganin mun bawa marada kunya a gasar da zata gudana a shekarar 2022,”

“Domin ganawar da mukai tsakanin masu ruwa da tsaki da mai horar da tawagar har mada ‘yan kwamitin tawagar, tattaunawar da mukai matuka ta kasance gwanin ban sha’awa,” a cewar Amaju Pinncik.

Tawagar Super Eagles dai na yunkurin kasancewa cikin kasashe biyar da zasu wakilci nahiyar afrika domin buga gasar kofin duniya a kasar kasar a shekarar 2022 da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!