Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Europa League: Barcelona da Napoli sun tashi wasa 1-1

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona daga kasar Spain, tayi kunnan doki daya da daya da tawagar Napoli ta kasar Italiya a gasar Europa League.

Fafatawar dai ta gudana a ranar Alhamis 17 ga Fabrairun 2022 a filin wasa na Camp Nou mallakin tawagar Barcelona.

Alkalin wasa Kovacs I. (Rou) ne dai ya jagoranci wasan da kungiyoyin biyu suka raba maki tsakaninsu.

Dan wasa Zielinski P ne dai ya fara zura kwallon farko a minti na 29 da wasan.

Kafin daga bisani matashin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ferren Torres ya warware kwallon a minti na 59 a bugun daga kai sai mai tsaran gida.

Barcelona dai ta gaza ci gaba da kasance a gasar cin kofin zakarun Champions League sakamakon ficewa da tai a matakin rukuni a gasar.

Wanda hakan ya bata damar kasancewa a gasar Europa League mai daraja ta biyu a nahiyar turai ta kakar wasannin shekarar 2022/2022.

Zuwa yanzu dai Barcelona zata ziyarci Napoli a kasar Italiya a ranar 24 ga watan da muke ciki na Fabrairu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!