Connect with us

Labaran Wasanni

SWAN Kano : Ta kafa kwamitin shirya gasar Kofin kafafen yada Labarai

Published

on

Kungiyar marubuta Labaran wasanni ta kasa reshen jihar Kano SWAN, ta kafa kwamitin shirya gasar ‘Local Organising Committee-LOC ‘, kofin kwallon kafa na kafafen yada Labarai dake jihar , wato ‘Inter Media Cup 2021’.

Kwamitin na dauke da alhakin shirya gasar da tsare -tsaren da suka kamata, don tabbatar da cewar an gudanar da Kofin na shekarar bana 2021, tare da kammala shi Lafiya.

Daga cikin ‘yan Kwamitin gudanarwar (LOC),sun hada da …

1.Abubakar Kwaru, daga Gidan Talabijin ma ARTV, a matsayin shugaba

2. Sai Salisu Basso na Jaridar Triumph, mataimakin shugaba

3. Da Aminu Halilu na Freedom Radio, a matsayin Sakatare

4.Abbati Sabo daga hukumar wasanni ta Kano KSSC, Jami’i

5. Auwalu Salisu daga Talabijin na NTA, Jami’i

6.Muzamil Dalha Yola na Aminchi Radio, Jami’i

7.Zainab Kundila daga Radio Kano, Jami’a

8.Mukthari Adana, daga ma’aikatar yada Labarai Jami’i

9.Salisu Babangida, daga ma’aikatar yada Labarai Jami’i.

10 Abba Tangalash na Vision Fm, Jami’i

11. Mohammed Nur daga Kamfanin Dillacin Labarai na kasa NAN, Jami’i

Sanarwar kafa kwamitin mai dauke da sa hannun Sakataren kungiyar ta SWAN, Abdulgafar Oladimeji, ta bukaci ‘yan Kwamitin da suyi aiki tukuru, wajen ganin anyi tare da kammala gasar cikin Nasara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!