Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

Ta’addanci: an kashe matashi a bakin sana’arsa

Published

on

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan fashi da makami ne sun hallaka wani matashi a jihar Neja.

Rahotani sun tabbatar da cewa matashin mai suna Auwalu Muhammad, dan asalin Gumel ne a jihar Jigawa.

Ana zargin ‘yan fashin sun kasha mutumi tare da tserewa da babur din sa da yake Sana’a da shi.

Idris Aliyu wanda shi ne Mai gidan marigayin, ya shaidawa manema labarai cewa “Auwal ya dauki fasinjoji ne zuwa yankin Tapa a jihar Neja, inda suka shammace shi wajen yi masa mummunan rauni kansa da wasu sassan jikinsa tare da jansa zuwa cikin daji suka kashe shi”.

“Sai dai abin takaicin da muka ga gawar mun lura da cewa an dade da kashe shi, amma har zuwa lokacin jami’an tsaro ba su iya gano shi ba, har sai da muka je da kan mu” a cewar Idris Aliyu.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim ya ruwaito rundunar ‘yan sandan jihar Neja bata yi karin bayani kan faruwar lamarin ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!