Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ta’addanci : An yi awon gaba da ma’aikatan jami’ar Ahmadu Bello

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sunyi awon gaba da wasu ma’aikatan jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Lamarin dai ya faru da misalign karfe daya na ranar yau Litinin inda maharani suka mamaye jami’ar tare da harfi a kan iska.

Jaridar Punch ta rawaito cewa maharani sun saki mutum biyu daga cikin mutanan da suka sace bayan da suka yi arangama da ‘yan sanda.

Daraktan Hulda da Jama’a na Jami’ar ta Ahmadu Bello, Malam Auwalu Umar, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau.

Sanarwar ta ce an yi musayar wuta tsakanin masu garkuwar da jami’an‘ yan sandan wanda hakan yasa suka bar harabar makarantar.
nan gaba kadan zamuje jami’ar kai tsaye danjin halin da ake ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!