Labarai
Taimakon kai-da-kai shi ne mafi a’ala ga manoma – Kungiyan manoma ta Kano
Shugaban kungiyar masu sarafa kayayyakin noma na jihar kano Alhaji Sadik Dan gaske ya ja hankalin manoma da su mai da hankali wajen taimakawa kan su da kayan noma masu inganci a jihar nan.
Alhaji Sadik dan gaske yace sun bude ofishinsu ne domin su taimakwa manoma masu safara kayan noma da kuma masu korafi akan wanda ake cinye musu kayan noma da gwamnati ta basu.
Ya kara da cewa wannan taro ne da yake nunawa cewa, wannan kungiya ta kara bunkasa a nan kano jihar kano da kuma yadda kungiyoyi ke bin dokokin da kungiya ta shinfida musu domin kare musu kayan noman da suka girba.
A nasa jawabun sakataren kunguyar ta kasa reshen jihar kano Alhaji Abdulmutallif sSulaiman ya ce sun zo Kano ne domin su kaddamar da ofishin masu safaran kayan noma da kuma tallafawa gwamnati da wasu ayyuka na noma a kasar nan baki daya.
An bude sabbin filayen noman rani a jami’ar Bayero
Manoman jihar Kano sun mayar wa da CBN amfanin gona
Hukumomi sun gaza samar da mafita kan noman rani -Garba Gidan Maza
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa, shuwagabannin kungiyar suna kira da gwamnatin tarraya da sauran jihohin kasar nan dasu rika aikawa da kayan noma zuwa ofishin hukumar domin inganta harkokin noma a kasar nan