Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun sauya wa wasu manyan jami’an ‘yan sanda wurin aiki – Sifeton ‘yan sanda

Published

on

Sifeto Janar na ‘yan sandan kasar nan Muhammed Adamu ya amince da yiwa wasu manyan jami’an rundunar sauyin wajen aiki.

Hakan na cikin wata sanarwar ce mai dauke da sa hannun mai magana da yawn rundunar DCP Frank Mba.

Sanarwar ta ce, cikin wadanda aka yiwa sauyin wajen aikin sun hada da: DIG Sanusi Lemu wanda ya koma sashen gudanar da ayyuka sai kuma AIG Usman Baba da ya koma mai rikon mukamin sashen kula da mulki da kudi na rundunar.

A cewar sanarwar dai, sauyin wajen aikin da aka yiwa manyan jami’an yana alaka ne da ritaya da DIG Abdulmajid Ali da kuma DIG Abduldahiru Danwawu su ka yi.

Haka zalika sufeto na ‘yan sandan ya kuma amince da nada AIG Mustapha Dandaura a matsayin sakataren rundunar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!