Labarai
Takaita amfani da layukan waya zai karfafa tsaro- Hadi Zarewa
Tsohon mataimakin sufeton ‘yan sandan kasar nan Muhammad Hadi Zarewa mai ritaya ya bayyana shirin nan na gwamnatin tarayya kan yadda za’a takaita mallakar layukan waya a hannun ‘yan Najeriya da cewa zai taimaka wajen kyautata tsaron kasar nan.
Muhammad Hadi Zarewa mai ritaya ya bayyana hakan ne ta cikin shirin duniyar mu a yau, na nan tashar freedom radiyo wanda ya mayar da hankall kan shirin takaita mallakar layukan waya a hannun jama’a.
Ya ce, tsarin ba zai sa mu karbuwa ba, har sai gwamnonin jahohi sun bada goyon bayan su wajen hana al’ummar da suke jagoranta mallakar layukan musamman ma ta hanyar sayar da su barkatai.
Amfani da fasahar zamani zai taimaka wajen magance matsalar tsaro -Dakta Sani Lawan Malumfashi
Kaduna za ta karbi tsarin tsaro na AMOTEKUN
Rundunar ‘yan sanda ta samar da tsaro don tunkarar zaben da za’a a Kano
Shi kuwa masanin kimiyyar sadarwa anan Kano, Malam Yusuf Ibrahim Sharada ya alakanta mallakar layukan waya sama da uku da cewa, yana da alaka da yin amfani da DATA wanda hakan ke sawa mutane na mallakar layuka da yawa.
Shi kuwa lauya mai zaman kansa a nan Kano Barisata Sale Muhammad Turmizi da ya kasance cikin shirin cewa yayi, idan har ana so dokar tayi amfani to sai an bi ka’ idodin da tun da fari ya kamata abi su kafin damar mallakar layukan wayar ya yawaita a hannun jama’a.
Dukkanin bakin sun bukaci da a tabbatar da wannan tsari na takaita mallakar layukan waya sama da uku a hannun al’umma wanda suka ce hakan zai taimaka wajen samun magance barazanar tsaro da gano masu aikata laifuka