Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnan Kano Abba Gida-Gida ya Ayyana Yau A Matsayin Ranar Hutu

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana yau laraba 4 ga watan Oktoba 2023 a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin tunawa da ranar haihuwar ma’aiki SAW

Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hutun ta bakin kwashinan yaɗa labarai Baba Halilu Ɗantiye cikin wata takarda da Kwamishinan ya fitar ya kuma rabawa manema labarai

Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya kuma shawarci al’umma jihar Kano da suyi koyi da irin ɗabi’un ma’aiki da sauran Sahabban sa a kowanne lokaci domin neman tsira

Ka zalika ya kuma bukaci al’umma da su kasance masu yin addu’a musamman kan tsananin matsin rayuwa da Samar da zaman lafiya a faɗin jihar Kano dama ƙasa baki ɗaya

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!