Connect with us

Labarai

Dalilan da zai sanya a sake yin nazarin komawa makarantu a Najeriya

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ce, zata sake yin nazari kan komawa makarantu da za’a yi a ranar 18 ga watan Janairun ne, kasancewar ana yawan samun karuwar masu  dauke da cutar Korona a kasar nan a kullum.

Ministan Ilimi  Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan  lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ya yin zaman kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar Corona.

Malam Adamu Adamu ya danganta wannan matakin da gwamnati zata dauka na sake yin nazarin  komawa makarantu a kasar nan da dawowar cutar Corona a karo na biyu wanda ake fama da shi  a Najeriya a halin yanzu da ma duniya baki daya.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, Ministan Ilimin na cewa, bude makarantu a wannan lokacin bai dace ba, la’akari da yadda adadin masu dauke da cutar ke karuwa a kullum wanda hakan ke sanya fargaba a zukantan ‘yan Najeriya.

Corona : Yau dalibai ke shiga mako na biyu da komawa makaranta a Kano

Buhari ya gargadi ‘yan Najeriya da su guji yiwa kan su gwajin Corona

Freedom Rediyo wata makaranta ce mai zaman kanta – Ambasada Sani Bala

Akan haka ne Malam Adamu Adamu ya ce gwamnati ta yanke shawarar komawa makarantun ne a  ranar 18 ga wannan wata a matsayin gwaji ko kuma manufa da aka tsara don cimma nasara.

Sai dai ya ce Gwamanati na kula da abubuwan da ke afkowa a cikin al’umma, a don haka ya zama wajibi a sake yin nazari kan komawa makarantu a Najeriya

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!