Connect with us

Labarai

Tallafin Corona: An dakatar da kwamandan Hisbah na Dala

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta dakatar da kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Dala Suyuɗi Hassan Muhammad.

Jami’in yaɗa labaran hukumar Ibrahim Lawal Fagge ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio.

Fagge ya ce, babban kwamandan hukumar Hisbah na jiha ne ya dakatar da shi har tsawon wata guda.

Dakatarwar ta biyo bayan zargin salwantar da kayan tallafin Corona da aka bayar domin rabawa al’umma.

A ranar Juma’a ne aka yi zama da ɓangarorin masu ƙorafi domin kawo dai-dai-to ga me da lamarin, amma aka tashi baram-baram.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!