Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Tambuwal ga Buhari: Muna son a sanya dokar ta ɓaci a jihar Sokoto

Published

on

Gwamna jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yayi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya sanya dokar ta ɓaci a dukkanin yankunan da suka fi fuskantar matsalar tsaro a jihar.

Gwamna Tambuwal ya bayyana hakan a ganawar da yayi da shugaba Buhari a daren ranar Litinin a fadarsa.

Tambuwal ya buƙaci shugaban ya baiwa rundunar sojin ƙasar nan damar gudanar da ayyukansu ba tare da ƙaƙƙautawa ba a dukkanin yankunan da lamarin ya shafa.

Bayanin hakan na cikin sanarwar da mai baiwa gwamnan Sokoto shawara kan harkokin yaɗa labarai Muhammad Bello ya fitar.

Wannan dai ya biyo bayan yadda jihar Sokoton ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a kwanakin nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!