Labarai
Tambuwal ya jajanta wa mazauna Jabo bisa harin sojin Amurka

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya jajanta wa al’ummar gundumar Jabo, bayan harin da rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar sojojin Amurka suka kai kan ‘yan ta’adda a yankin.
Aminu Tambuwal ya mika sakon jajen nasa ne yayin wata ziyara da ya kai yankin, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da jajanta wa mutanen da abin ya shafa.
Sanatan ya jaddada cewa ta’addanci ba batun addini ko kabila ba ne, illa barazana ce ga kowa da kowa, tare da bukatar jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai.
You must be logged in to post a comment Login