Connect with us

Labarai

Tambuwal : manoma ku koma bakin aiki zamu kawo karshen ‘yan bindiga

Published

on

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya umarci manoman yankin da ‘yan bindiga suka lalata, da su koma bakin aikin su, yana mai tabbatar musu da cewa a yanzu gwamnatin jiha da ta tarayya zasu yi duk mai yiwuwa don kawo karshen tashe tashen hankula a jihar.

Kazalika Tambuwal ya bukaci manoman da su baiwa jami’an tsaro hadin kai a lokacin da suke gudanar da ayyuakan su a sassan jihar.

A baya-baya nan ne dai ‘yan sandan suka yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga 3 tare da cafke mutum 2 yayin wani sumame da uka kaiwa yan bindigar.

Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana damuwar sa kan yadda ayyukan yan ta’adda ya addabi jihar ta yadda yayi sanadiyyar dakatar da ayyukan manoma wanda hakan ya janyo karancin abinci ga al’ummar jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 330,185 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!