Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Taraba:Darius Ishaku na jam’iyyar PDP ya lashe zabe

Published

on

Dan takarar jam’iyyar PDP a jihar Taraba, Darius Ishaku ya lashe zaben Gwamnan jihar da ya gudana a ranar Asabar din data gabata da kuri’u 520,433 kamar yadda jami’in tattara sakamaon zaben jihar Farfesa Shehu Iya na jami’ar Adamawa ya bayyana, yayin da abokin takarar sa na jam’iyyar APC Sani Danladi, ya samu kuri’a 362,735.

Shima dan takarar Jam’iyyar PDP a jihar Imo Emeka Ihedioha, ya lashe zaben Gwamnan jihar daya gudana a ranar Asabar da kuri’u 273,404 kamar yadda baturan zaben jihar ta Imo Mr. Francis Chukwuemeka Otonta ya bayyana.

A wani bangare kuma jam’iyyar APC ta ki amin cewa da zaben gwamnoni dana yan majalisu na yankin kudu masao kudan cin kasar nan da suka hadar da jihar  Akwa Ibom, da Cross River da Delta.

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin kudu maso kudancin kasar nan Ntufam Eta ne ya bayyana hakan yayin da ke zantawa da manema labarai a jiya, inda ya kalubalan ci zabukan da suka gudana a yankunan da cewa ba’a yisu yadda ya kamata ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!