Adabin Hausa
Tarihin hawan Dorayi a Kano
Hawan Dorayi, ya samo asali ne tun zamanin sarkin kano Abdullahi Bayero inda tarihi ya nuna cewa kafin zuwa dorayi sarki kan je garin gogel da fanda da kuma takai duk a lakacin bikin karamar sallah.
Sai dai sakamakon shekarun da suka cimma marigayi sarkin kano Alhaji Abdullahi Bayero ya sanya aka gina gidansa na dorayi wanda shi ne gandun sarki a yanzu.
Haka kuma tarihi ya nuna cewa duk sarakunan da suka biyo bayan marigayi Alhaji Abdullahi Bayero sun yi wannan hawa na dorayi don dabbaka al’adar masarautar kano.
A tarihi dai sarki kan fito ne da sanyin safiya ta kofar kwaru zuwa warure zuwa aisami zuwa gwauron dutse ya wuce zuwa kofar famfo sannan yabi ta tal’udu zuwa kwanar FCE sannan ya mike zuwa dorayi.
Wajen dawowa kuma yana biyowa ta mandawari ne sannan ya shige gida ta kofar kudu inda da wannan hawa na dorayi ne kuma ake kammala bukukuwan sallah karama a birnin kano.
Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login