Labaran Kano
Tarihin Sarkin Kano na 15 a Daular Fulani Alhaji Aminu Ado Bayero
An haifi Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1961 a Kano, kuma shi ne Sarkin Kano na 15 a Daular Fulani, inda gwamnatin jihar Kano ta nada shi a ranar 9 ga watan Maris din shekarar 2020, bayan sauke Sarkin Kano na 14 a Daular Fulani Muhammadu Sanusi na biyu a ranar 9 ga watan Maris shekarar 2020.
Mahaifinsa Alhaji Ado Bayero ya yi sarautar Kano daga shekarar 1963 zuwa 2014, wanda ya rasu a ranar 6 ga watan Yunin shekarar 2014.
Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne ‘da na biyu ga Alhaji Ado Bayero, ya yi karatun alku’ani mai girma da na fikihu a gidan Sarki, kuma ya yi makarantar Furamare a kofar Kudu sannan ya zarce zuwa Kwalejin gwamnati ta Birnin Kudu.
Ya yi digirinsa na farko a kan aikin jarida a Jami’ar Bayero ta Kano, ya kuma yi aikin hidimar kasa na shekara guda a gidan Talabijin na Kasa NTA da ke garin Makurdi na jihar Benue. Sannan ya tafi makarantar koyon tukin jirgin sama ta Flying College da ke Oakland a Jihar Carlifonia ta Kasar Amurka.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi aiki a matsayin jami’in hulda da jama’a na Kamfanin sufurin Jiragen sama na Kabo Air, sannan daga bisani ya zama injiniya a sashen direbobin jirgin sama.
A shekarar 1990 ne Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya nada Aminu Ado Bayero a matsayin Dan Majen Kano kuma Hakimin Dala, kafin daga likkafarsa zuwa Dan Buram Kano a cikin watan Oktoban shekarar ta 1990.
A shekarar 1992 ne aka nada shi a matsayin Turakin Kano sannan a shekarar 2000 ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida. Ya kuma taba zama shugaban kwmaitin shirya Hawan Daba na fadar Sarkin Kano.
A shekarar 2014 ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya daga likkafarsa zuwa Wamban Kano, kuma Hakimin Birni. A shekarar 2019 ne gwamnatin Jihar Kano ta nada Alhaji Aminu Bayero a matsayin Sarkin Bichi, kuma a ranar 9 ga watan Maris shekarar 2020 ne gwamnatin Kano ta nada Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15 a Daular Fulani.
You must be logged in to post a comment Login