Kasuwanci
Taron tattalin arziƙi: Mun daina dogara da man fetur – Buhari
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ta mayar da hankali kan rage dogaro da arziƙin man fetir.
Shugaban ya ce, ya zuwa yanzu Najeriya ta mayar da hankali kan inganta harkokin noma da fasahar sadarwa da kuma ma’adinai.
Sannan ya ce, ta mayar da hankali kan yaƙi da cin hanci da rashawa da matsalolin tsaro da sauyin yanayi da ƙaddamar da shirin tallafawa al’umma.
Buhari ya bayyana hakan yayin taron saka hannun jari da ake gudanarwa a ƙasar Saudiyya karo na 5.
Taron wanda dama ce ta gabatar da buƙatu da suka shafi harkokin tattalin arziki, wanda za a shafe tsawon kwanaki 4 ana gabatar da shi a birnin Riyadh.
Kazalika taron ya ƙunshi shugabannin ƙasashe da manyan ƴan kasuwa masu saka hannun jari da bankuna.
You must be logged in to post a comment Login