Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Tashin Dala ne ya sanya mu ƙara kudin Hajji- NAHCON

Published

on

Hukumar kula da aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON, ta ce, tsadar canja Naira zuwa Dalar Amurka ce ta sanya ta kara kudin kujerar aikin Hajjin bana sakamakon cewa, da Dalar Amurkan ake biyan kujerun.

Mai magana da yawun hukumar Hajiya Fatima Sanda Usara, ce ta bayyana hakan ga Freedom Radio a yau.

Fatima Sanda ta ce, lokacin da NAHCON ta kayyade farashin kudin kujerar aikin Hajjin bana, ana canzar da Dala akan naira dari takwas zuwa dari tara, amma yanzu ta haura hakan.

Fatima Sanda Usara, ta ƙara da cewa, hukumar NAHCON ta sanya ranar Alhamis mai zuwa watau 28 ga watan da muke ciki a matsayin ranar da duk mai sha’awar zuwa aikin Hajji zai biya musamman wadanda zasu cika sauran kudaden su, idan kuma basu da Ikon biya to su rubuta takarda zuwa NAHCON din domin shirya dawo musu da kudadensu.

Har ya zuwa yanzu dai ba a kai ga cike guraben kujeru sama da dubu casa’in da shida da hukumar kula da aikin Hajji da Umarah ta ƙasar Saudiyya ta ware wa maniyyatan Nijeriya ba.

Da yammacin jiya Lahadi ne Hukumar ta jin daɗin Alhazan Nijeriya NAHCON bayyana cewa duk ɗan ƙasar da ya biya kuɗin aikin Hajjin bana, Sai ya cika naira miliyan daya da dubu dari tara da sha takwas 1,918,032.91 nan da kwanaki hudu.

Sai dai wannan al’umma na ta bayyana damuwa bisa yadda kuɗin aikin Hajjin ya kama har Naira Miliyan 6 da dubu ɗari 8.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!