Labarai
Tashin farashin tikitin jirgi a Disamba ba shi da alaka da haraji- NCAA

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasa NCAA ta bayyana cewa tashin farashin tikitin jirgin sama da aka samu a watan Disamba, ba shi da alaka da wani sabon haraji ko karin kudin gwamnati.
NCAA ta ce hauhawar farashin ya samo asali ne daga karuwar bukatar tafiye-tafiye a lokacin bukukuwan karshen shekara, tare da kalubalen kudin aiki da kamfanonin jiragen sama ke fuskanta, ciki har da tsadar man jirgi, kula da jirage da sauyin farashin musayar kudi.
Hukumar ta kuma ce ba ta amince da kara haraji ko wasu kudade a wannan lokaci ba, inda ta ce tana ci gaba da sa ido domin tabbatar da adalci a farashin tikitin jirgin.
You must be logged in to post a comment Login