Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Akwai bukatar bibiyar tarihin marigayi Janar Murtala Muhammad-Walin Kano

Published

on

Walin Kano kuma makusanci ga tsohon shugaban mulkin soja na kasar nan, Janar Murtala Ramat Muhammad, Alhaji Mahe Bashir, ya bayyana salon mulki na marigayin a matsayin wanda ke cike da gaskiya da rikon amana.

Alhaji Mahe Bashir Wali wanda tsohon mukaddashin Sufeto Janar na yan sandan kasar nan ne, ya bayyana hakan  yayin tattaunawa da Freedom Radio, a wani bangare na tunawa da ranar da aka kashe marigayi Janar Murtala.

Ya ce, ranar na da matukar muhimmanci a tarihin kasar nan, duba da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasar nan a yayin da ya ke mulki.

Alhaji Mahe Bashir Wali ya kara da cewa, akwai bukatar al’umma da sauran matasa na wannan lokaci, su rika bibiyar tarihin marigayin, a wani mataki na kwai-kwayar halayen sa na son ci gaba da kuma gaskiya da rikon amana.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!