Siyasa
Tattalin arziki yana kara bunkasa sakamakon rufe kan iyakoki –Hafizu Kawu
Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Tarauni Hafizu kawu ya bayyana cewa, tattalin arzikin Najeriya na dab da bunkasa duk da kukan da wasu ke yi bisa rufe kan iyakokin hasar nan.
Hafizu Kawun dai ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Kowane Gauta na nan Freedom Radio.
Ya ce akwai yiwuwar tattalin arzikin ya bunkasa sakamakon daukar matakan da gwamnatin tarayya ta yi a fannoni da dama.
Ya kara da cewa, babban bankin kasa CBN ya fitar da rahoton cewa nan da shekara mai kamawa tattalin arzikin kasa zai habaka bisa yadda aka dakatar da shigo da wasu kayayyaki inda harkokin noma za su kara inganta.
Ya kara da cewa, binciken na CBN ya bayyana cewa duk shekara ‘yan Najeriya na shigo da shinkafa ta kimanin dala biliyan 5, inda yanzu haka noman shinkafa ya fara habaka sakamakon dakatar da shigo da shinkafar.
RUBUTU MASU ALAKA:
Babu banbanci tsakanin jam’iyyun APC da PDP –Bashir Jantile
Muntari Ishaq ya can-can ci zama kwamishina -Aminu Mai dawa
Siyasa: Muntari bai can-canci zama kwamishina ba –Hamza Darma