Connect with us

Labarai

Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 4.0

Published

on

Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, , ya bayyana farin cikinsa kan yadda tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 4.07 cikin ɗari a zangon ƙarshe na shekarar 2025.

Sabon rahoton da ta fitar ya nuna cewa bunƙasar ta samo asali ne daga manyan sassa uku na tattalin arziki — noma, masana’antu da ayyukan hidima.

A cewar ministan, noma ya girma da kashi 4.0%, masana’antu sun ƙaru da 3.88%, yayin da ɓangaren ayyukan hidima ya jagoranci da kashi 4.15%. Ya ce wannan na nuni da cewa bunƙasar tattalin arzikin na da tushe mai faɗi, ba a takaita ta a ɓangare guda ba.

Edun ya kuma bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu cikin shekara goma da bunƙasar tattalin arziki ta wuce kashi 4%, baya ga lokacin farfaɗowar bayan annobar COVID-19. Ya ƙara da cewa a duk shekarar 2025 baki ɗaya, tattalin arzikin ya girma da kashi 3.87%, inda girman sa ya kai naira tiriliyan 441.5.

Ministan ya danganta wannan nasara da kyakkyawan tsari a harkokin kuɗi da kuma gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin Shugaba ke aiwatarwa.

Rahoton ya kuma nuna cewa fiye da ƙananan fannoni 30 sun samu bunƙasa sama da kashi 3%, lamarin da ke ƙara nuna faɗaɗar tattalin arzikin ƙasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!