Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a shekarar 2021 – IMF

Published

on

Asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya ce, tattalin arzikin Najeriya zai samu bunkasar akalla kaso biyu da digo biyar a wannan shekara ta dubu biyu da shirin da daya.

 

Wannan sabon alkaluman sun zarce hasashen da asusun na IMF ya yi tun da fari a watan Janairu da ke cewa, tattalin arzikin na Najeriya zai karu da kaso daya ne da digo biyar kacal a shekarar ta dubu biyu da ashirin da daya.

 

Asusun na IMF da ke da zama a birnin Washington DC da ke kasar Amurka ya fitar da wannan rahoto ne na watan afrilu a yau talata.

 

Ko a wani rahoto da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a watan shekaran jiya na Fabrairu, ta ce, Najeriya ta fita daga kangin matsin tattalin arziki da ta shiga a shekarar da ta gabata, inda a zangon karshe na shekarar 2020 tattalin arzikin Najeriyar ya samu tagomashin kasa da kashi daya.

 

NBS ta kuma yi hasashen cewa, tattalin arzikin Najeriya zai karu da kaso uku da digo hudu a wannan shekarar.

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!