Barka Da Hantsi
Tattaunawa kan matsalolin shigowa da gurbataccen Man Fetur a Najeriya
A cikin shirin na wannan ranar, an yin duba ne ga batun matsalar shigowa da gurɓataccen Man fetur da kuma sauran matsaloli dake kewaye da sha’anin hada-hadar Man fetur ɗin a Najeriya.
Baƙin da da aka tattauna dasu sun haɗa da Comrade Isah Tijjani tsohon mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC, kuma tsohon Muƙaddashin shugaban ƙungiyar ma’aikatan Man fetur da iskar Gas ta ƙasa NUPENG. Sai kuma Amanallahi Ahmad Muhammad, masani kan siyasar tattalin arziƙi, kuma masanin kan hada-hadar man fetur a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login