Ƙetare
Tattaunawa ta da shugaba Putin a waya ta yi amfani sosai- Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tattaunawar da ya yi da shugaban Rasha Vladimir Putin ta waya ta yi amfani sosai, a ci gaba da ƙokarin da yake yi na sasanta rikici tsakanin Ukraine da Rasha.
Bayan kammala wayar, Trump ya ce sun amince a yi wata ganawa tsakanin manyan jami’an gwamnatin Rasha da Amurka a mako mai zuwa, kafin daga baya kuma a yi wata ganawar ta gaba da gaba a ƙasar Hungary.
An yi tattaunawar ta waya ne kwana ɗaya gabanin ziyarar da shugaban Ukraine Volodimyr Zelensky zai kai ziyara zuwa Amurka a yau Juma’a domin neman ƙarin tallafi.
You must be logged in to post a comment Login