Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

TINUBU GA BUHARI: Sai ka tashi tsaye domin jama’a na fama da talauci

Published

on

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya ce, duk da cewa kasar nan ta fice daga kangin mashash-sharan tattalin arziki da ta shiga a baya, amma har yanzu tattalin arzikin Nigeria na cikin mawuyacin hali.

Madugun jam’iyyar ta APC ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke gabatar da mukala a wajen taron lakca don tunawa da Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello wanda ya gudana yau asabar a garin Kaduna.

Tsohon gwamnan jihar ta Lagos ya ce duk da cewa gwamnatin shugaba Buhari ta yi namijin kokari wajen fitar da Nigeria daga mawuyacin halin da ta shiga, amma har yanzu da sauran rina a kaba.

Saboda haka a cewar Tinubu akwai bukatar shugaban kasar ya kara daura damara don rage radadin talauci da jama’a ke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!