Labarai
Tinubu ya gana da shugaban rundunar sojin AFRICOM

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin shugaban rundunar sojin Amurka ta Afirka AFRICOM, Janar Dagvin Anderson, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara tattaunawa kan haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka, musamman wajen yaƙi da ta’addanci da sauran barazanar tsaro a yankin.
Yayin taron, Janar Anderson ya zo ne tare da tawagar AFRICOM da ta haɗa da Muƙaddashin Jakadan Amurka a kasar nan , Keith Heffern, Babban Mai Ba da Shawara kan Harkokin Waje na AFRICOM, Ambasada Peter Vrooman.
Shugaba Tinubu ya karɓi tawagar tare da manyan jami’an gwamnatin sa da suka haɗa da Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Ƙasa, Nuhu Ribadu, Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu.
You must be logged in to post a comment Login