Labarai
Tinubu ya gana da shuwagabannin NLC a Abuja

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu, ya gana da shugabannin Kungiyar Kwadago ta kasa NLC a Fadar mulki ta Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja a daren Talatar makon nan, a wani yunkuri na dakatar da shirin zanga-zanga a fadin kasar nan da ƙungiyar ta shirya yi kan matsalar rashin tsaro.
Rahotonni sun bayyana cewa, NLC ta sanar da shirya zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a yau 17 ga Disamba, inda ta danganta hakan da abin da ta kira taɓarɓarewar halin tsaro a ƙasar nan.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ne ya jagoranci shugabannin ƙungiyar zuwa taron.
Bayan kammala taron, Ajaero bai bayyana matsayarsu ba kan zanga-zangar, inda NLC din ta ce, za ta sanar da matsayarta kafin gobe Alhamis.
Sai dai tun da safiyar yau Laraba ne aka gudanar da zanga-zangar a jihohin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login