Labarai
Tinubu ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawa da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP, wanda da ake kallon ta a matsayin yunkurin kulla sabon hadin kan siyasa kafin babban zaben shekarar 2027.
Ganawar ta gudana ne a Fadar Shugaban kasa da ke Aso Rock, inda Ministan Abuja, Nyesom Wike ya jagoranci jiga-jigan zuwa wajen shugaban.
Wannan ganawa ta kunshi abokan siyasa na kusa da Wike musamman mambobin tsohuwar kungiyar gwamnonin G5, wato wadanda suka yi adawa da takarar Atiku Abubakar a zaben 2023.
Wadanda suka halarci ganawar sun hada Ayodele Fayose tsohon gwamnan Jihar Ekiti da Samuel Ortom tsohon Gwamnan Jihar Benue da kuma Okezie Ikpeazu tsohon gwamnan Jihar Abia.
You must be logged in to post a comment Login