Labarai
Tinubu ya zargi MDD da yin watsi da matsalolin da duniya ke fuskanta

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci Majalisar Dinkin Duniya da ta canja salo idan har ta na son ci gaba da kasancewa mai tasiri a duniya.
Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da mataimakinsa, Kashim Shettima, ya gabatar a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a birnin New York, inda ya zargi Majalisar da yin watsi da ainihin matsalolin da duniya ke fuskanta.
Shugaban ya nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da harkokin Majalisar da kuma jinkirin da ake samu wajen kawo ƙarshen rikice-rikicen kasa da kasa, musamman rikicin Falasɗinu.
Haka kuma shugaba Tinubu ya ce, rashin tsayin daka wajen ɗaukar mataki akan irin wadannan rikice-rikice ya zama babbar matsala ga rayuwar mutane da ya jaddada cewa mafita ta dindindin ga Falasdinu ita ce tsarin kafa ƙasashe biyu domin tabbatar da zaman lafiya.
Shugaban ya kuma sake jaddada buƙatar Najeriya ta samu kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya na mai cewa dole a sabunta tsarin domin ya dace da halin da duniya take ciki a yanzu.
You must be logged in to post a comment Login