Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tokyo Olympics: ‘Yan wasan Najeriya na shiri cikin natsuwa – Sunday Dare

Published

on

Ministan matasa da wasanni Sunday Dare, ya ce, tawagar ‘yan wasan da su wakilci Najeriya a gasar Olympics ta 2020 da za ayi a birnin Tokyo da ke kasar Japan na cigaba da shiryawa wasannin a tsanake.

Dare ya bayyana haka ne ga manema labarai a wani taron kwanaki biyu da hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa ta gudanar a jami’ar fasaha ta Akure da ke jihar Ondo.

Ya kuma ce, “Shirye-shirye na cigaba da kankama a mataki daban-daban sai dai wasu daga cikinsu ba za ka iya samun su a jaridu ko a kafafen yada labarai ba.”

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kamfanin Dilancin Labarai na kasa NAN, ya ce, an tsaiya da ranar 23 ga watan Yulin 2021 a matsayin ranar da za a fara gasar ta 2020 Olympics a kuma karkare a ranar 8 ga watan Augusta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!