Labaran Wasanni
Tottenham ta sallami mai horar da ita Nuno Santo Espirito
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2021/11/prito.jpg)
Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham da ke kasar Ingila ta sanar da sallamar mai horar da tawagar Nuno Espirito Santo, bayan watanni hudu daya kwashe yana jagorantar kungiyar.
Tottenham dai a karshen mako ta yi rashin nasara da ci 3-0 a hannun Manchester United a gasar Firimiya.
Kungiyar Spurs ta yi rashin nasara a wasanni 5 cikin 7 da ta buga.
Inda ta ke da maki 8 da tazarar maki 10 tsakaninta da mai jagorantar teburin gasar Chelsea.
“Mun dauki matakin sallamar Nuno ne sakamakon yadda kungiyar ta mu a yanzu ta gaza samun nasararori, amma dai munsan irin gudunmawar da ya bayar a cigaban kungiyar a cewar daraktan wasannin na kungiyar Fabio Paratici.
Mai shekaru 47 dan kasar Portugal tin da fari ya amince da kwantaragin shekaru biyu a kungiyar
bayan shafe shekaru hudu ya na jagorantar Wolves.
Kungiyar kwallon kafa ta Totttenham dai ta ayyana cewa sallamar mai horar da kungiyar shine matakin da zai kawo mata nasarori a anan gaba.
You must be logged in to post a comment Login