Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Bana sha’awar horar da Barcelona – Mikel Arteta

Published

on

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta ya ce ba ya sha’awar horar da Barcelona.

Wanda tuni rahotanni suka bayyana ya na cikin masu horarwa da ka iya jagorantar Barcelona.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar ta sallami Ronald Koeman a matsayin mai horar da ita a makon da ya gabata.

Jumulla Barcelona a kakar wasannin da muke ciki ta yi rashin nasara a wasanni 4 cikin 6 da ta buga a baya-bayannan.

Koeman ya fara jagorantar kungiyar Barcelona a watan Agustan shekarar 2020 da a lokacin ne Barcelona ta lashe gasar Copa del Rey.

Arteta wanda tsohon dan wasan matasan kungiyar Barcelona ne tuni rahotanni suka bayyana ana saran ka iya zama mai horar da kungiyar kafin daga bisani ya nuna kin amincewarsa da jagorantar kungiyar.

” Akwai abu da yawa sun fari a shekarun baya ciki kuwa har da barin Lionel Messi kungiyar wanda kowa ya san shine ruhin kungiyar,”

A yanzu dai B Sergi Barjuan ne zai ci gaba da jagorantar kungiyar kafin maye gurbin wanda zai jagoranci tawagar a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!