Labarai
Transparency international:akwai bukatar gudanar da binciken karbar na goro da ake zargin gwamnan Kano
Kungiyar kasa da kasa da ke yaki da cin hanci da rashawa wato transparency international, ta bukaci da a gudanar da bincike da babu hannun gwamnati a ciki, kan zargin karbar na goro da ake yiwa gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Shugaban kungiyar a nan Najeriya Auwal Musa Rafsanjani ne ya bayyana haka yayin zantawa da jaridar Solacebase a Abuja.
Ya ce gudanar da bincike ba tare da sanya bakin gwamnati ba, zai taimaka gaya wajen yaki da ake da cin hanci da rashawa a kasar nan.
Shugaban kungiyar ta Transparency International a nan Najeriya, ya kuma ce, kwamitin da majalisar dokokin Kano ta kafa kan batun, ba zai iya gudanar da aikin sa bisa gaskiya da adalci ba.
Kungiyar ta Transparency International ta bakin shugaban ta Auwal Musa Rafsanjani, ta kuma bukaci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya sauka daga mukamin sa don gudun tsoma bakin sa a cikin binciken da ake yi a kansa.
A cewar kungiyar ba zai yiwu gwamnan ya zama mai laifi kuma ya zamo alkali ba, saboda alakar sa da ‘yan majalisu, ba zai sa suyi aiki bisa gaskiya da adalci ba.