Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

Trump ya ƙirƙiro sabon dandalin sada zumunta na kansa

Published

on

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirin ƙaddamar da dandalin sada zumunta a internet na ƙashin kan sa.

Samar da dandalin zai mayar da hankali wajen ganin ya samu damar aikewa da sakonnin sa bayan da kamfanonin twitter da Facebook suka dakatar da shi, sakamakon harin da magoya bayan sa suka kai majalisar dokokin Amurka.

Tsohon shugaban yace kamfanin yaɗa labaran sa na TMTG ne zai mallaki dandalin wanda ya yiwa suna ‘TRUTH Social’, kuma ana saran zai fara aikin karɓar baƙi daga watan gobe, yayin da ake iya samun manhajar sa a intanet domin amfani da shi.

Trump yace ya kirkiro dandalin ’TRUTH Social da TMTG’ domin ƙalubalantar kama karyar da yace manyan kamfanonin sadarwar duniya irin su Facebook da twitter ke yi.

Tsohon shugaban ya bayyana cewar, yayin da ƙungiyar Taliban ke amfani da twitter sosai, sai ga shi an hana shugaban Amurka mafi farin jini, inda yake cewa ba za su amince da haka ba.

Trump ya dade yana sukar kamfanonin sada zumuntar saboda matakan da suke ɗauka akan sa na yaɗa labaran karya waɗanda suka ce ya saɓawa dokokin su.

Ɗaukar matakin dakatar da tsohon shugaban ya harzuƙa shi, musamman lokacin da yake ta bada labaran cewar shi ne ya samu nasarar zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a Amurka bara, bayan hukumar zaɓe da majalisar dokoki sun tabbatar da cewar ya sha kaye.

Wannan matsayi nasa, ya sa magoya bayan sa kai hari majalisar dokokin, abinda yayi sanadiyar rasa rayuka da dama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!