Ƙetare
Trump ya bai wa Pentagon umarnin fara shirin ɗaukar matakin soji kan Najeriya

Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa, ya bai wa ma’aikatar Tsaron kasarsa (Pentagon) umarni kan ta fara shirin ɗaukar matakin soji kan Najeriya, bisa zargin da ya ke yi yin kisan kiyashi ga mabiya addinin Kirista.
Trump ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya sake maimaita tuhumarsa ga gwamnatin Najeriya kan cin zarafin mabiya addinin kirista, zargi da gwamnatin Najeriya ke musantawa akai-akai, tana mai cewa ƙasar na kare ‘yan ƙasa ba tare da nuna bambanci na addini ba.
A halin yanzu dai, gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ido kan wannan furuci, tare da tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakai don kare mutuncin ƙasar da tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’umma masu mabambantan addinai.
You must be logged in to post a comment Login